Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMutane 200 sun mutu a wurin haƙar ma'adinai a Congo

Mutane 200 sun mutu a wurin haƙar ma’adinai a Congo

Kimanin mutane 200 ne suka mutu a wurin hakar ma’adanai

Rahotanni sun bayyana cewa sama da mutane 200 ne suka mutu sakamakon ruftawar wasu wuraren hakar ma’adanai a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyya Kongo.

Kakakin gwamnan lardin Arewacin Kivu da ‘yan tawaye suka nada, ya ce wadanda abin ya shafa sun hada da masu hakar ma’adinai, da yara da mata.

Ya bayyana cewa, an ceto wasu daga cikinsu.

Wurin dai yana samar da kusan kashi 15 cikin 100 na ma’adanin coltan na duniya, wanda yake da matuƙar muhimmanci ga samar da wayoyin hannu da sauran kayan lantarki.

Haka zalika wajan yana ƙarƙashin ikon ƙungiyar ƴan tawaye ta M23 tun shekarar 2024.

Mutane sama da miliyan ɗaya da rabi ne ke aiki a irin waɗannan wurare da ba a amince da su ba, inda haɗurra irin waɗannan suka zamo ruwan dare.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments