Kasar Iran ta mayar da martani ga barazanar Amurka na cewa za a kawo mata hari idan ba a cika wasu sharudda ba.
Shugaba Trump ya ce yana son kauce wa ƙaddamar da harin soja a kan Iran, ko da yake al’amura na iya sauyawa idan har Iran din ta ci gaba da shirinta na Nukiliya.
Ya shaida wa ‘yan jarida a birnin Washington cewa zai yi magana da Iran din.
Iran dai ta yi barazanar duk wanda ya ce kule, za ta ce masa cas.
Wani babban jami’in sojan kasar Birgediya Janar Mohammad Akraminia, ya ce karfin sojinsu, ta kai su iya kai hari kan duk wani sansanin sojin Amurkar da ke gabas ta tsakiya.
Da farko Shugaba Trump ya yi gargaɗin cewa sojojin Amurkar za su kai hari idan Iran ta kashe fararen hula da ke zanga-zangar adawa da gwamnati ne, kafin daga bisani ya sauya tunani.