Gwamnatin Sojin Jamhuriyyar Nijar ta zargi ƙasashen Faransa da Benin da kuma Ivory Coast da ɗaukar nauyin harin filin jirgin saman birnin Yamai yayin da gwamnatin ta kuma godewa Rasha wadda ta ce da taimakonta ne aka daƙile yunƙurin harin.
Janar Abdourahamane Tiani, wanda ya ƙwaci mulkin ƙasar bayan hamɓarar da gwamnatin farar hula a juyin mulkin da ya jagoranta cikin watan Yulin 2023, ya yi wannan zargi ne a jawabin da ya gabatar ta gidan talabijin a ranar Alhamis, 29 ga watan Janairu, 2026.
Shugaban ya ce shugaba Emmanuel Macron na Faransa da Patrice Talon na Benin da kuma Alassane Ouattara na Ivory Coast su ke da hannu wajen kitsa kai wannan hari da ya tashi hankalin jama’ar birnin na Yamar.
Kamar yadda kafofin yaɗa labarai na ciki da wajen Nijar suka ruwaito, jagoran mulkin Sojin bai bayar da kowacce hujja don mara baya ga iƙirarin nasa wajen tabbatar da hannun ƙasashen 3 a wannan hari ba.
Tun bayan wannan jawabi na daren jiya Alhamis, ilahirin ƙasashen 3 babu ko guda da ta mayar da martani ko kuma tsokaci kan iƙirarin na jagoran gwamnatin Sojin ta Nijar.
Kafin wannan zargi daga Abderrahman Tchiani, sai da jagoran mulkin Sojin ya ziyarci filin jirgin saman Diori Hamani da hare-haren suka faru wanda ke da tazarar kilomita 10 daga fadar gwamnatin ƙasar.
A daren Laraba ne dai aka riƙa juyo ƙarar musayar bindiga da kuma fashewar wasu abubuwa da ake kyautata zaton bom ne a filin jirgin wanda ministan tsaro Salifou Modi ya ce an ɗauki tsawon mintuna 30 gabanin nasarar daƙile harin.
Ministan tsaron na Nijar ya ce yayin wannan hare-hare wanda dakarunsu da taimakon Rasha suka mayar da martani da ruwan harsasai ta sama tare da daƙile ƴan ta’addan, Sojojin ƙasar 4 sun samu raunuka yayinda suka yi nasarar kashe maharan aƙalla 20 ciki har da wasu Faransawa.
Wasu kafofin labarai a jamhuriyyar ta Nijar sun ruwaito cewa an kama wasu mutane 7 da ransu a cikin maharan.