Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sama da mutane miliyan 3 da yaƙin da aka shafe kusan shekaru 3 ana gwabzawa a Sudan ya ɗaiɗaita sun koma gidajensu, duk da yadda ake cigaba da fuskantar mummunan rikici a sassan ƙasar.
A cikin wani rahoto da ta fitar a jiya Litinin, Hukumar ta ce mutane kimanin 300,300,000, waɗanda suka gudu sakamakon yaƙin ne suka kom a’a gida tun daga watan Nuwamba, 2025.
Tun a watan Afrilun shekarar 2023 ne Sudan ta faɗa yaƙi, biyo bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin rundunar sojin ƙasar da dakarun kai ɗaukin gaggawa na RSF.
Yaƙin dai ya yi sanadin mutuwar dubban mutane kana ya haddasa abin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana a matsayin matsalar jinƙai mafi girma a duniya, bayan da ya ɗaiɗaita mutane kimanin miliyan 14 a ciki da wajen ƙasar.
Ƙaruwar masu komawa gida ya biyo bayan hare-hare ba ƙaƙƙautawa da sojin Sudan ta tsananta ne a ƙarshen shekarar 2024, inda ta sake ƙwace ikon yankunan tsakiyar ƙasa daga hannun RSF.
Hukumar kula da ƙaurar baƙi ta IOM ta ce sama kashi 3 cikin hudu na masu komawa gida, sun fito ne daga sansanonin ƴan gudun hijira na cikin gida, a myayin fda kashi 17 suka yi balaguro daga ƙasashen waje.