Matatar Man Ɗangote ta sanar da ƙarin farashin N100 kan kowacce litar man fetur guda inda a yanzu ta sanar da cewa za ta koma sayar da man akan farashin N799.
Tun daga ranar 12 ga watan Disamban, 2025 matatar ke sayar da kowacce litar man guda kan farashin N699 sai dai a wata sanarwa da ta fitar a jiya Litinin, ta ce farashin ya sauya nan ta ke.
Sanarwar matatar ta ce gidajen manta na MRS za su koma sayar da kowacce lita guda a farashin N839 daga N739 da suke sayarwa a baya.
Sanarwar ta Ɗangote ta ce tun farko an zaftare farashin ne saboda bukukuwan Kirsimati da sabuwar shekara, kuma bayan ƙarƙarewar wannan bukukuwa farashin zai dawo yadda ya ke a baya.
Matatar ta jaddada cewa za ta ci gaba da aiki tuƙuri wajen daidaita farashin man tare da tabbatar da wadatuwarsa a sassan ƙasar.