Najeriya ta sake fuskantar katsewar wutar lantarki sakamakon lalacewar babban layin lantarki ƙasar a ranar Talata.
Wannan shi ne karo na biyu da babban layin wutar ke fuskantar irin wannan matsala a shekarar 2026 wanda ya haifar da katsewar wutar lantarki a fannoni da dama na ƙasar.
Layin wutar ya fara lalacewa ne a ranar Juma’ar da ta gabata.
Bincike ya nuna cewa dukkanin tashoshin samar da wutar lantarki 23 da ke haɗe da babban layin sun daina aiki gaba ɗaya.
A halin yanzu dai, babu cikakken bayani kan abin da ya janyo wannan lalacewa.