Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKasar Sifaniya ta dakatar da shige da ficen jiragen ƙasa a Catalonia...

Kasar Sifaniya ta dakatar da shige da ficen jiragen ƙasa a Catalonia bayan mummunan hatsari

Hukumomi a Sifaniya sun dakatar da duk wata jigilar jiragen ƙasa a yankin Catalonia, bayan mummunan hatsarin da ya sake aukuwa a jiya Talata.

Hatsarin dai shi ne na biyu a cikin kwanaki uku a ƙasar, kuma hukumomi sun yi amanna cewa rashin yanayi mai kyau ke haifar da shi.

Mutum 37 ne suka samu rauni, huɗu daga cikin su kuma suna cikin mawuyacin hali, yayin da direban jirgin ya mutu.

Yankin Catalonia dai na cikin wuraren da gurɓatar yanayi ta yi ƙamari a Sifaniya a ƴan kwanakin nan.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments