Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiWasu ‘yan ta’adda sun kashe fiye da mutane 30 a Nijar

Wasu ‘yan ta’adda sun kashe fiye da mutane 30 a Nijar

Yan ta’adda sun kai hari tare da kashe akalla mutane 30 a Nijar

Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai hari tare da kashe aƙalla fararen hula 31 a wani ƙauye na Yammacin Nijar da ke da iyaka da Burkina Faso da Mali.

Majiyoyi sun ce ‘yan ta’addan da ake zargin dai sun kai hari ranar Lahadi a wani kauye da ke yankin Tillaberi, wanda ke yanki kan iyakoki uku – wani yanki da ke fuskantar tashin hankali inda iyakokin Nijar, Burkina Faso da Mali suka hadu waje guda.

Tsawon kusan shekaru goma, ‘yan ta’adda da ke da alaƙa da Al-Qaeda na kai munanan hare-hare a yankin.

“A ranar Lahadi ne dai yan bindiga ɗauke da makamai sun kashe mutane 31 daga cikin mazaunanmu a Bosiye; mutane 30 sun mutu nan take, kuma ɗaya daga cikin biyar da suka jikkata ya mutu a wata cibiyar kula da lafiya,” wani mazaunin yankin ya shaida wa AFP.

Wata ƙungiyar ɗalibai ta yankin ta kuma tabbatar da wannan adadin a cikin wata sanarwa, tana mai cewa ta yi matuƙar mamaki da baƙin ciki da wannan mummunan aiki na rashin imani.

A watan Satumba, a wani harin kwanton bauna an kashe magajin garin Gorouol wanda gwamnatin riƙon ƙwarya ta Nijar ta naɗa a yankin da Bosiye yake.

Yankin Tillaberi ya zama yanki mafi fuskanta hare-hare a tsakiyar Sahel a shekarar 2025, a cewar ACLED, wata ƙungiya mai zaman kanta da ke sa ido kan rikice-rikice.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments