Shafin sada zumunta na Elon Musk, X, ya sanar da wasu sabbin matakai da zai ɗauka don dakatar da manhajarsa ta fasahar Grok AI daga ƙirƙirar hotunan batsar mutane ba tare da neman amincewar su ba, musamman hotunan da ke bayyana surar mutane cikin kaya ko yanayi na sirri.
Ana ci gaba da samun suka daga sassan duniya kan yadda ake amfani da manhajar wajen ƙirƙirar hotunan batsa na mata da yara.
Sababbin matakan za su shafi duk masu amfani da shafin X, ciki har da waɗanda ke biyan kuɗin amfani da shi.
Matakin dai na zuwa ne bayan babban mai gabatar da ƙara a California ya bayyana cewa jihar za ta yi bincike kan yadda ake amfani da manhajar Grok wajen ƙirƙirar hotunan karya da kuma abubuwan da suka saɓa doka.