Jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya nuna damuwa matuƙa kan halin da siyasar jihar Kano ke ciki a yanzu.
Kwankwaso ya ce rikicin da ake fama da shi a siyasar Kano ba abin farin ciki ba ne, inda ya roƙi ’yan siyasa da su daina duk wani abu da ke ƙara rarrabuwar kai, su nemi hanyar da za a samu fahimta da zaman lafiya.
Ya bayyana cewa har yanzu, gwamnatin NNPP na da damar yi wa al’ummar Kano aiki, muddin aka samu haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin ’yan siyasa.
Sanatan ya ce abubuwan da ke faruwa a halin yanzu abin damuwa ne ƙwarai, yana mai cewa da ace mafarki ne, da ya fi masa sauƙi.
Kwankwaso ya kuma bayyana cewa ya gana da wasu manyan ’yan siyasa domin hana duk wani yunkuri da zai kawo cikas ga gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.
Duk da rikice-rikicen da ake fama da su, Kwankwaso ya jaddada cewa gwamnatin NNPP har yanzu tana da lokaci da damar cika alkawurran da ta dauka, idan aka samu haɗin kai da fahimta.
Ya ce kiran da ake yi na komawa jam’iyyar APC raini ne ga magoya bayan NNPP da suka sadaukar da lokacinsu da ƙarfinsu domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a Kano.
Kwankwaso ya kara da cewa magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya na cikin ƙalubale, amma duk da haka sun nuna haƙuri da jajircewa kan abin da suka yi imani da shi.
Ya gargadi masu matsin lamba kan sauya sheƙar Gwamnan Kano, yana mai cewa idan ana son hakan, to a bukace shi ya bar kujerar gwamna.