Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaA karo na biyu Gwamnan Kano ya canja lokacin komawa jam’iyyar APC

A karo na biyu Gwamnan Kano ya canja lokacin komawa jam’iyyar APC

Abba Kabir Yusuf ya sake daga lokacin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC

An samu sauyin shiri kan rahotannin da ke cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
‎
‎Majiyoyi da ke kusa da gwamnan sun ce ranar da aka fara tsarawa—Litinin, 5 ga Janairu, 2026 yanzu an mayar da ita Litinin, 12 ga Janairu, 2026, domin kammala shirye-shirye.
‎
‎Tun da farko, Rahotanni sun bayyana cewa Gwamna Yusuf zai sauya sheƙa a ranar 5 ga Janairu.

Sai dai sabon bayani ya nuna an ɗauki matakin dagewa ne saboda buƙatar ƙarin shawarwari.
‎
Daily Nigeria Hausa ta ruwaito cewa ‎wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce an cimma wannan matsaya ne bayan wani taro da Gwamna Yusuf ya yi da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a Abuja ranar Juma’a.

A cewar majiyar, gwamnan na neman ƙarin lokaci ne domin ƙara tuntubar ‘yan majalisar dokokin jihar da sauran manyan masu ruwa da tsaki a Kano, musamman waɗanda har yanzu ba su bayyana cikakken goyon bayansu ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments