A yau Asabar Shugaba Donald Trump ya sanar da cewa sojojin Amurka sun kama shugaban Venezuela Nicolas Maduro bayan sun kai wani babban hari a kan ƙasar da ke kudancin Amurka.
Shugaban Amurka da babbar murya ya na mai nuna jajircewar dakarun Amurka kusan ƴan kwanaki bayan da Nicolas Maduro ya bayyana kyaukiyawar fata na shiga tattaunawa da Amurka kan safarar miyagun kwayoyi da mai, bayan makonni da aka shafe Amurka na sa matsin lamba kan gwamnatinsa.
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na ƙasar Venezuela, Maduro ya ce a shirye yake ya shiga tattauna da Amurka “duk inda suke so da kuma duk lokacin da suke bukata.
Shugaban Amurka ya bayyana cewa “Amurka ta yi nasarar kai wani babban hari kan Venezuela da shugabanta, Shugaba Nicolas Maduro, wanda, tare da matarsa, aka kama su, yanzu haka an kama hanyar ficewa da su daga ƙasar” in ji Trump a shafinsa na Truth Social.
Trump ya ce zai yi taron manema labarai da misalin karfe 11:00 na safe (16:00 GMT) a gidansa da ke Mar-a-Lago a Florida.