Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeFiye da mutane 3,000 ne suka mutu yayin tsallaka teku zuwa Turai

Fiye da mutane 3,000 ne suka mutu yayin tsallaka teku zuwa Turai

Sama da mutane 3,000 ne suka mutu a yunkurin tsallakawa kasashen Turai

Sabbin alƙaluma sun nuna cewa fiye da mutane 3,000 ne suka rasa rayukansu yayin ƙoƙarin ƙetare teku zuwa ƙasar Spain a cikin shekarar 2025.

Wannan adadi ya ragu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, amma ƙungiyoyin kare hakkin bakin haure na gargaɗin cewa hakan ba yana nufin tafiyar ta zama mai aminci ba.

A cewar ƙungiyar sa-ido kan baƙin haure Caminando Fronteras, ta ce mutane 3,090 ne suka nutse a teku tsakanin Janairu zuwa tsakiyar Disambar 2025.

Rahoton ya nuna cewa cikin waɗanda suka mutu akwai mata 192 da kuma yara 437, lamarin da ke ƙara tayar da hankula game da haɗarin da ke tattare da wannan tafiya.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Spain ta ce baƙin haure kusan 36,000 ne suka shiga ƙasar ta teku da ƙasa ba bisa ƙa’ida ba a wannan lokaci.

Wannan adadi ya ragu sosai idan aka kwatanta da fiye da 60,000 da aka samu a shekarar da ta gabata, abin da hukumomi ke gani a matsayin ci gaba.

Gwamnati ta danganta raguwar da aka samu da tsauraran matakan tsaro a kan iyakoki, musamman a ƙasar Mauritania, wacce ke ɗaya daga cikin manyan wuraren tashin baƙin haure zuwa Spain.

A shekarar da ta gabata, Mauritania ta rattaba hannu kan yarjejeniyar kuɗin €210m da Tarayyar Turai domin daƙile yawan baƙin hauren da ke barin ƙasar.

Sai dai ƙungiyar kare hakkin ɗan Adam Human Rights Watch ta zargi hukumomin Mauritania da cin zarafin baƙin haure, ciki har da tashin hankali da muzantawa.

Gwamnatin Mauritania ta musanta waɗannan zarge-zarge gaba ɗaya, tana mai jaddada cewa ba ta aikata cin zarafi ga baƙin haure, duk da ci gaba da taƙaddama kan hanyoyin daƙile kwararar baƙin haure a yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments