Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTsananin zafi ne ya sa tukunyar gas ta fashe a babban asibitin...

Tsananin zafi ne ya sa tukunyar gas ta fashe a babban asibitin Kebbi – Yan sanda

Yan sanda sun tab tabbatar da cewa rana ce ta sa tunkuyar gas tai bindiga ba Bam ba

Rundunar yan sandan jihar Kebbi ta bayyana cewa fashewar da ta auku a Babban Asibitin Bagudo ba ta da alaƙa da bam ko wani hari.

A cewar rundunar, lamarin ya faru ne da safiyar ranar Talata, inda ya jefa al’umma cikin firgici, sai dai an tabbatar da cewa babu asarar rai.

Ta cikin sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar yan sandan jihar, SP Bashir Usman, ya fitar, ya ce fashewar ta samo asali ne daga gobara da ta haifar da zafin gas na na’urorin AC da firinji, wanda hakan ya haddasa karar fashewa da aka ji.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments