Kotu ta tasa keyar Malami da iyalinsa gidan yarin Kuje

Kotun Tarayya ta tsare Malami da matar sa da Dan sa gidan yarin kuje

0
173

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, tare da mai ɗakinsa da kuma ɗansa Abubakar Abdulaziz Malami a gidan yarin Kuje, bayan da suka ƙi amince wa da tuhume-tuhume 16 da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gabatar a kansu.

An gurfanar da su a gaban kotun a ranar Talata, inda suka bayyana ƙin amincewa da zargin da ya shafi safarar kuɗaɗen haramun da mallakar kadarori ba bisa ƙa’ida ba.

EFCC ta shigar da tuhume-tuhume 16 a kan Malami, ɗansa da Hajia Bashir Asabe, tana zargin su da safarar kuɗaɗe da kuma mallakar kadarori da darajarsu ta haura naira biliyan 8.7.

A cewar hukumar, ana zargin waɗanda ake tuhuma da amfani da asusun banki da dama tare da kamfanoni a tsawon kusan shekaru goma, domin mallakar kuɗaɗen da ake zargin sun samo su ta hanyoyin da ba su dace da doka ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here