Yawan mutanen da ake zartar wa da hukuncin kisa a Iran a shekarar nan na neman ninƙa yawan na bara har sau biyu.
Ƙungiyar rajin kare hakkin dan’adam ta Iran wadda ke Norway ta bayyana cewa ta tabbatar da ƙarin zartar da wannan haddi har 1,500 zuwa farkon watan nan na Disamba, inda aka zartar da wasu da dama tun kafin wannan lokacin.
A shekarar da ta gabata, ta ce ta iya tantance zartar da hukuncin kisa 975.
Ana samun ƙaruwar waɗanda ake zartar wa hukuncin kisan tun bayan zanga-zangar gama-gari da aka yi a karshen 2022.
Kusan kashi 90 cikin 100 na hukuncin kisan ko dai na kisan kai ne ko kuma laifi na miyagun ƙwayoyi.