Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaNa cancanta zama Shugaban Najeriya – Gwamna Seyi Makinde

Na cancanta zama Shugaban Najeriya – Gwamna Seyi Makinde

Gwamna Seyi Makinde ya bayyana ya cancanta ya zama Shugaban Najeriya, yayin da ya ke shirin tsayawa takara a 2027

Yayin da rahotanni ke ƙara bayyana kan aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya, gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya ce yana da dukkan abin da ake bukata na jagorantar ƙasar.

Makinde ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi daga wasu ‘yan jarida a wata tattaunawa da aka yi da shi a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ranar Talata.

Gwamnan ya alakanta wannan ikirari nasa da gogewarsa wajen jagorantar jihar Oyo da kuma tarihin aikinsa a fannin injiniyanci, a cewar rahoton Channels TV.

Makinde ya kuma soki yawaitar sauya sheƙa zuwa APC, yana cewa hakan na barazana ga dimokuraɗiyya da drukusa adawa a ƙasar.

Gwamnan ya bayyana cewa ba zai mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a 2027 ba, yana mai cewa zai mayar da hankali kan ƙarfafa PDP.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments