Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiA gaggauta kwashe jami’an dake gidan Aminu Ado na Nasarrawa – Kwankwaso...

A gaggauta kwashe jami’an dake gidan Aminu Ado na Nasarrawa – Kwankwaso ga ƴan sanda

Rabi’u Musa Kwankwaso ya gargadi Kwamishinan yan sandan Kano da ya kwashe jami’an dake gidan Aminu Ado Bayero na Nassarawa

Tsohon ɗan takarar Shugaban Ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi kira ga kwamishinan ƴan sandan jihar Kano da ya janye jami’an tsaron dake gadin Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero a gidan Sarki na Nasarawa

Kwankwaso ya yi kiran ne a yayin da yake jawabi a matsayin babban bako na musamman a bikin kaddamar da jami’an tsaron unguwanni da gwamnatin Kano ta samar.

Acewar Kwankwaso, Sarki Sanusi ne kadai halastaccen Sarkin Kano.

Sannan ya yi Allah-wadai da waɗanda ya zarga da ajiye Sarki Aminu Ado Bayero a gidan Sarki na Nasarawa inda ya kira shi da matsayin “makabarta”.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments