Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS) ta ce ta kama kwantena 20 da aka karkatar ba bisa ka’ida ba, masu darajar harajin da aka biya (DPV) N769.53 miliyan, a yankin Kwastam na Kano/Jigawa.
Babban Kwanturola na Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a gidan Kwastam da ke Kano.
Ya ce an yi wannan kamun ne tsakanin zangon biyu zuwa na huɗu na shekarar 2025, a wani bangare na ƙara tsaurara matakai kan karkatar da kaya.
Adeniyi ya bayyana cewa an tanadi kwantenan ne domin a kai su tashoshin cikin gida da yankunan cinikayya na musamman, amma aka karkatar da su ba bisa ka’ida ba.
Ya ce hakan ya saɓa wa Sashe na 64(b) na Dokar Hukumar Kwastam ta Nijeriya, 2023.
A cewarsa, karkatar da kaya na janyo asarar kudin shiga ga gwamnati tare da haifar da barazana ga tsaro.
Kayan da aka samu a cikin kwantena
Kayan da aka kama sun hada da kwantena bakwai na tayal masu darajar N228.58m, da kwantena biyu na man dizal na injina masu darajar N87.56m.
Haka kuma akwai kwantena biyu na kayan ‘polyester’ masu darajar N77.99m, da kwantena daya na tsofaffin tufafi mai darajar N48.42m.
Sauran sun hada da kwantena hudu na yaduka da leshi masu darajar N226.15m, kwantena daya na ruwan Zamzam da aka haramta mai darajar N21.46m, da kwantena uku na kayan kiwon lafiya da yaduddukan leshi masu darajar N25.2m.
Adeniyi ya ce Hukumar Kwastam na fara amfani da na’urorin bibiya na zamani a fadin kasar domin sa ido kan motsin kwantena.
Ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu da laifi, ciki har da jami’an Kwastam, zai fuskanci gurfanarwa, kwace kaya, da tsauraran hukunci.
Ya bukaci masu shigo da kaya da dillalan jigilar kaya su bi dokokin Kwastam, yana mai jaddada cewa hukumar na goyon bayan halastaccen kasuwanci, amma ba za ta lamunci fasa-kwauri da karkatar da kaya ba.