Wasu fusattattun mazauna garin Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru a Jihar Zamfara sun kai hari ga wani dan majalisar dokokin jihar a ranar Laraba.
Dan majalisar shi ne Kabiru Mikailu, wakilin mazabar Maru ta Kudu a Majalisar Dokokin Jihar Zamfara.
Mazauna sun ce bayan ya ci zabe bai kula da su ba. Sun ce bai rika ziyartar al’umma ba, bai halarci bukukuwan Sallah ba, kuma bai kai ziyara ko jajantawa iyalan da hare-haren ‘yan bindiga suka shafa ba.
Lamarin ya faru ne lokacin da dan majalisar ya raka Gwamna Dauda Lawal zuwa garin domin wata ziyara ta aiki. Daga bisani jami’an tsaro sun shiga tsakani domin kwantar da hankula da hana rikici ya kara tsananta.
Gwamna ya kai ziyara domin kaddamar da ayyuka
Gwamna Dauda Lawal ya ziyarci Dansadau ne domin kaddamar da aikin sake gina hanyar Dansadau–Gusau mai tsawon fiye da kilomita 90.
Haka kuma ya bayar da umarnin gyara da sabunta Babban Asibitin garin, tare da samar da wutar lantarki ta hasken rana.
Gwamnan ya tabbatar wa mazauna cewa gwamnatinsa na kokarin dawo da tsaro, sake gina muhimman abubuwan more rayuwa, da kuma tallafa wa al’ummomin da matsalar tsaro ta shafa a fadin Jihar Zamfara.
A yayin ziyarar, Sarkin Dansadau, Alhaji Garba Muhammad, ya nada Gwamna Lawal da sarautar gargajiya ta Garkuwan Dansadau.