A yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalolin rashin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya wanda hakan ke tayar da hankulan jama’a Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawo karshen matsalar.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a jihar Legas, ranar Litinin, 15 ga watan Disamban 2025 yayin da ya bude taron shekara-shekara na babban hafsan sojojin kasa na 2025.
Tinubu ya bayyana shirin da gwamnatinsa ke yi domin cewa kwanciyar hankali ya dawo zukatan ‘yan Najeriya
Shugaba Tinubu ya nuna cewa gwamnatinsa za ta hada dukkan kayan aikin sojoji da hukumomin tsaro domin murkushe barazanar tsaro da kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa a fadin Najeriya.