Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaWasu yan bindiga sun sace mutane huɗu tare da jikkata 3 a...

Wasu yan bindiga sun sace mutane huɗu tare da jikkata 3 a Kano

‘Yan bindiga sunyi awon gaba da wasu mutane hudu tare da jikkata uku.

’Yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Lakwaya da ke ƙaramar hukumar Gwarzo a Jihar Kano a daren Lahadi da misalin karfe 10.00 na dare, inda suka sace mutum huɗu tare da jikkata wasu uku.

Mai unguwar Namandala, Babangida Bello ne ya tabbatar da afkuwan lamarin inda ya ce ƴan bindigan kusan 30 ne suka kutsa ƙauyen.

Ya bayyana cewa:

“Cikin mutum huɗu ɗin da yan bindigan suka ce, guda biyu samu sun tsere.”.

Ya ƙara da cewa ƴan bindigan sun sace garken dabbobi guda hudu daga unguwar.

Ya kuma ce nan take aka sanar da jami’an tsaro, kuma sun kawo ɗauki a cikin gaggawa.

Wannan hari ƙari ne ga wasu hare-hare da ’yan bindiga suka yi a baya-bayan nan a jihar, waɗanda suka yi sanadiyar asarar rayuka da garkuwa da mutane.

Rahotanni sun nuna cewa, kananan hukumomi akalla uku a Arewacin jihar da ke maƙwabta da Jihar Katsina sun fuskanci hare-hare irin wannan.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments