Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGobara ta kone kasuwar katako kurmus a Jihar Gombe

Gobara ta kone kasuwar katako kurmus a Jihar Gombe

Wata gobara ta lakume kasuwar Katako da ke Gombe

Wata gobara ta tashi a kasuwar katako da ke yankin tashar jirgin ƙasa a birnin Gombe, inda ta ƙone shaguna da kayayyaki masu yawa, lamarin da ya janyo babbar asara ga ‘yan kasuwa da dama.

Gobarar ta faru ne a daren Litinin, bayan ‘yan kasuwa sun rufe kasuwancinsu, kuma ta durƙusar da sana’o’in mutanen da ke dogaro da kasuwar wajen samun abin rayuwa.

Gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana alhini da jimami matuƙa bisa faruwar lamarin.

A cikin wata sanarwa da Darakta-Janar na harkokin yaɗa labarai na gwamnatin jihar, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi da juyayi ga al’ummar da abin ya shafa, tare da miƙa saƙon jaje ga dukkan ‘yan kasuwa da masu shagunan da gobarar ta rutsa da su.

Sanarwar ta ce “Gwamna Inuwa ya tabbatar wa waɗanda abin ya shafa cewa gwamnatin jihar na tare da su a wannan lokaci mai wahala, inda ya umarci hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar SEMA da sauran hukumomi masu alaƙa da su da su hanzarta bincike kan musabbabin gobarar, tare da kai tallafi da agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa.

Gwamnan ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kafa wata cibiyar kwana-kwana ta zamani mai kayan aiki na ƙwarewa domin ƙarfafa kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments