Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeMutane 8 sun mutu a hare-haren sojojin Amurka bisa zargin jiragen da...

Mutane 8 sun mutu a hare-haren sojojin Amurka bisa zargin jiragen da safarar kwayoyi.

Wasu mutane takwas sun mutu sakamakon hare-haren Amurka kan zargin jiragen da safarar kwayoyi.

Sojojin Amurka sun ce sun kai hare-hare kan jiragen ruwa uku da ake zargi da safarar ƙwayoyi a Tekun Pacific, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum takwas.

Rundunar sojin kudancin Amurka ta wallafa faifan bidiyon hare-haren a shafukan sada zumunta, inda ta ce jiragen na tafiya ne ta hanyoyin da aka san ana safarar miyagun ƙwayoyi, kuma suna cikin ayyukan safarar kwayoyi.

A cewar sojojin, sama da jiragen ruwa 20 a Tekun Pasifik da na Caribbean aka kai wa hare-hare a ‘yan watannin nan, inda aƙalla mutum 90 suka rasa rayukansu.

Wannan wani ɓangare ne na tsaurara matakan da shugaba Donald Trump ke ɗauka kan ƙungiyoyin da yake zargi da safarar kwayoyi zuwa yankin.

A martaninta, Fadar White House ta ce matakan da aka ɗauka sun yi daidai da dokokin yaƙi, domin kare Amurka daga kungiyoyin safarar kwayoyi da take zargin suna kokarin “shigar da guba zuwa kasar da lalata rayukan ‘yan ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments