Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroIna da hujjoji a kan zargin da na yi wa Matawalle -...

Ina da hujjoji a kan zargin da na yi wa Matawalle – Sheikh Asada

Malamin ya ce sakonsa ya kai Fadar Shugaban Ƙasa, kuma a shirye ya ke ya je kotu da hujjoji game da zargin da ya yi wa Matawalle

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Murtala Asada, ya sake nanata zarge-zargen da ya daɗe yana yi kan Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle. Ya ce an kai sakonsa har Fadar Shugaban Ƙasa.

Wannan ya biyo bayan wata hira da Matawalle ya yi, inda ya ce duk wanda ke zarginsa da alaƙa da ‘yan ta’adda ya kai shi kotu. A wani rubutu da aka wallafa a shafin X, Sheikh Asada ya ce Matawalle ya tura wani tsohon kwamishinansa domin ya mayar da martani kan zarge-zargen.

Sheikh Asada ya ce ko da yake an ji Bello Turji ya fito yana musanta zargin, hakan bai sa ya janye maganganunsa ba. Ya bayyana cewa ba sabon abu ba ne, domin tun lokacin da Matawalle yake gwamnan Zamfara yake fadin irin wadannan zarge-zarge.

Malamin ya ce ya kalli wani bidiyo da Matawalle ke magana a kai, inda aka ambaci raba abincin dabbobi ga ‘yan bindiga a lokacin tattaunawar zaman lafiya. Ya ce dole Matawalle ya fito ya amsa tambayoyi kan abin da ake zarginsa da shi.

Sheikh Asada ya kuma ce yana shirye ya je kotu domin kare kansa, yana mai cewa yana da hujjoji da zai gabatar. Ya zargi Matawalle da kokarin hana Musa Kamarawa zuwa kotu a matsayin shaida, tare da yi masa alkawarin taimako.

Har ila yau, malamin ya sake zargin cewa Matawalle ya sayi motoci ga wasu fitattun ‘yan bindiga. A gefe guda kuma, Sheikh Ahmad Gumi ya taba kare Matawalle, yana cewa ya fahimci matsalolin tsaro kuma ya yi kokarin magance su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments