Ajaero ya bayyana haka ne jim kadan bayan wata ziyarar girmamawa da ya kai wa shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa 19 kuma gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, a Abuja.
NLC ta ce sace-sace da kisan gilla sun addabi ma’aikata, don haka ta bukaci gwamnati ta dauki kwararan matakai don kawo karshen matsalar
A cewar Joe Ajaero, ‘yan kwadago za su gudanar da zanga-zangar domin tilasta wa gwamnati daukar kwararan matakai kan matsalar tsaro da ke addabar ƙasar, a cewar rahoton Channels TV.
Shugaban ‘yan kwadago ya kuma jaddada cewa yanzu matsalar tsaro na shafar kowane ɗan Najeriya, ba tare da la’akari da matsayi, kabila ko addini ba.
Ajaero ya ce rashin tsaro na lalata tattalin arzikin ƙasa tare da raunana damar Najeriya na jawo hankalin masu zuba jari na cikin gida da na ƙasashen waje.
Ya ce:
“Zanga-zangar da muke shirin yi na da nufin jawo hankalin gwamnati kan yadda rashin tsaro ke shafar masu zuba jari da ma’aikata, wadanda ake sacewa kullum, wasu ma ana kashe su.”