Kotun Koli ta Najeriya ta tabbatar da hukuncin kisa da aka yanke wa Maryam Sanda, surukar tsohon shugaban PDP, saboda laifin kashe mijinta.
A ranar 27 ga watan Janairu, 2020, babbar kotun Abuja ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same ta da laifin caka wa mijinta, Bilyamin Bello, wuka har lahira a gidansu da ke Abuja a 2017.
Ko da yake ta shafe kusan shekara shida da watanni takwas a gidan yari na Suleja, Shugaba Bola Tinubu ya sassauta mata hukunci zuwa zaman gidan yari na shekaru 12 bisa ikon da Kundin tsarin mulki ya ba shi na yi wa masu laifi afuwa.
Dalilan Tinubu na yi wa Maryam Sanda afuwa
Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi (SAN), ya bayyana cewa an saka sunan Maryam Sanda a cikin jerin wadanda aka yi wa afuwa ne bisa “dalilan tausayi da kuma kare muradun ’ya’yanta.”
Ya ce kyawawan halayenta a gidan yari, sake salon rayuwa, zama abin koyi ga wasu fursunoni da nuna nadama ne suka sa aka yi mata rangwame.
A yayin da aka ci gaba da shari’a, wani kwamitin alkalai biyar na Kotun Koli, ya samu rinjaye da mutum 4:1, inda aka sake tabbatar da hukuncin da aka yanke mata na kisa ta hanyar rataya.
Dalilin kotu na soke afuwar shugaban ƙasa
Kotun ta ce dukkannin hujjojin da Maryam ta gabatar don neman soke hukuncin ba su da tushe, ta kuma kori daukaka karar da ta shigar saboda rashin cancanta.
A cikin hukuncin da Justice Moore Adumein ya jagoranta, kotun ta ce masu gabatar da kara sun tabbatar da laifinta da hujjoju kwarara.
Kotun Koli ta ce hukuncin kotun daukaka kara da ya tabbatar da hukuncin farko ba shi da wata matsala.
A ƙarshe, Kotun Koli ta bayyana cewa ba daidai ba ne don Shugaba Tinubu ya yi yunkurin bayar da afuwa a karar da har yanzu tana gaban kotu, musamman ma da ta shafi laifin kashe mutum.