Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiKotu ta tsare tsohon ministan ƙwadago Chris Ngige gidan yari

Kotu ta tsare tsohon ministan ƙwadago Chris Ngige gidan yari

Wata babbar kotun tarayya mai a garin Gwarimpa da ke babban birnin tarayya Abuja ta tura tsohon ministan ƙwadago Chris Ngige gidan yarin Kuje.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ce ta gurfanar da tsohon Ministan a gaban mai shari’a Mariam Hassan bisa tuhume-tuhume guda takwas da suka danganci cin hanci da rashawa.

Ngige, wanda ya kasance Minista a zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya isa harabar kotun ne da misalin ƙarfe 8:10 na safiyar Juma’a, 12 ga watan Disamba, 2025 tare da rakiyar jami’an EFCC.

Hukumar ta zargi Ngige da aikata laifuffukan ne a lokacin da yake Minista, musamman a lokacin da yake kula da hukumar bayar da tallafi ta Najeriya wato NSITF.

A tuhuma ta farko, ana zargin cewa daga Satumban 2015 zuwa Mayun 2023, Ngige ya yi amfani da tsohon matsayinsa na Minista wajen bai wa abokansa cin gajiyar kwangila ba bisa ka’ida.

Sai dai a zaman kotun, tsohon ministan ya musanta laifukan da ake tuhumarsa da su.

Mai shari’a Mariam ta ɗage shari’ar zuwa Litinin domin sauraron buƙatar neman belinsa, sannan ta bayar da umarni a tsare shi a gidan yarin Kuje har zuwa ranar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments