Amurka dai ta dauki matakin ne kwana daya bayan ta kwace wani jirgin ruwa na dakon mai a gabar tekun Venezuelar.
Kuma tuni fadar gwamnatin Amurkar ta ce za ta kwashe man da ke cikin jirgin.
Yayin da yake ci gaba da matsin lamba a kan Shugaba Maduro Trump ya nuna alamun cewa nan gaba kadan Amurka za ta fara kai hari kan mutanen da take zargi na safarar miyagun kwayoyi ta kasa.
Shugaba na Venezuela ya ce, ainahin burin shugaba Trump shi ne sauyin gwamnati, yana son kawar da shi ne daga mulki