Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanciARCON ta fara tantance Iconic Digital Media

ARCON ta fara tantance Iconic Digital Media

Hukumar kula da tallace-tallace ta Najeriya ta gana da mahukuntan Iconic digital media a Legas

Hukumar kula da tallace-tallace ta Najeriya (ARCON) ta kai ziyartar ga kamfanin Iconic Digital Media Services and Advertisement a Legas.

Hukumar ta kai ziyarar ne a ranar Juma’a domin duba ka’idojin samun lasisin gudanar da ayyukan talla da gudanar da harkokin kamfanin.

Wannan na ƙunshe a cikin bayanan da Iconic Digital Media Services and Advertisement Company ta fitar.

Ziyarar ta ƙunshi kwamitin tantancewa na musamman daga ARCON, wanda ya tattauna da hukumomin kamfanin game da bin ƙa’idodin aiki, tsarin gudanarwa, da sauran batutuwa na aikin kamfanin.

Wannan ziyara dai wani muhimmin mataki ne na tabbatar da cewa dukkanin cibiyoyin tallace-tallace da kamfanonin dijital a Najeriya na aiki bisa ƙa’ida, tare da ingantaccen tsari da ya dace da dokokin ARCON.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments