Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaDa taimakona ka zama gwamna – Marafa ya yi martani ga Matawalle

Da taimakona ka zama gwamna – Marafa ya yi martani ga Matawalle

Marafa Support Group ta ce akwai lokacin da Matawalle ya yi alkawarin ba zai ci amanar Marafa ba.

Sanata Kabiru Garba Marafa ya maida martani ga ikirarin Ƙaramjn Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle, wanda ya ce ya taɓa taimaka wa Marafa lokacin da yake gwamnan Zamfara.

Marafa ya ce wannan magana ba gaskiya ba ce, saboda shi ne ya ɗauki nauyin Matawalle har ya samu kujerar gwamna a 2019.

A wata sanarwa da Shugaban Marafa Support Group, Alhaji Surajo Garba Maikatako, ya fitar, ya ce furucin Matawalle, da Tukur Danfulani, shugaban APC na jihar, cewa sun taimaka wa Marafa, karya ce tsagwaronta.

Maikatako ya ce ba za su yarda a sauya tarihi ba, saboda ko a takaitaccen tarihin siyasar Zamfara, duk wanda ya amfana da gwamnatin Matawalle ya amfana ne sakamakon gudunmawar Sanata Marafa.

Ya ƙara da cewa Matawalle da kansa ya taɓa tabbatar da cewa Marafa ne ya taimaka masa, har ma ya yi alƙawarin ba zai ci amana ba.

Ya yi tambaya cewa:

“Ta yaya za a ce muna yi muku hassada? Me za mu yi kishi da shi alhali mu muka kafa tsarin da ya kai su ga mulki?

Maikatako ya ce ikirarin Danfulani cewa mutane suna yi masu hassada abin dariya ne, domin ba za a yi kishi da abin da kai ka kirkira ba.

Ya ce Tukur Danfulani da ubangidansa Matawalle sun gaza a siyasa, sun gaza a mu'amala, yanzu ma sun gaza wajen faɗin gaskiya kan tushen nasararsu.

Ya yi zargin cewa akwai matsaloli da ake jingina wa Matawalle daga manyan majiyoyi, kuma har yanzu bai tunkari kotu ya kare kansa ba.

Shugaban Marafa Support Group ya roki magoya bayan Sanata Marafa su ci gaba da kasancewa masu nutsuwa, su kuma kare akidojin siyasar Marafa ta hanyar bin doka da oda.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments