Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTsohon shugaban Benin Boni, yayi Allah wadai da yunƙurin juyin mulki a...

Tsohon shugaban Benin Boni, yayi Allah wadai da yunƙurin juyin mulki a ƙasar

Thomas Boni tsohon shugaban Benin ya bayyana takaicin sa kan yunkurin juyin mulki a kasar

Tsohon shugaban Jamhuriyar Benin Thomas Boni Yayi, ya yi tir da Allah-wadai da yunƙurin kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya ta ƙasar.

Boni Yayi ya ce a matsayinsa na wanda ya samu damar mulkin Benin tsawon shekaru 10, ba zai taɓa yarda da yi amfani da ƙarfi don ƙwace mulki ba.

Ya ce ya bi diddigin abubuwan da suka faru a ƙasar, kuma tuni ya umarci jam’iyyarsa ta Democrat da ta gaggauta fitar sanarwar yin tir da duk wani yunƙurin ƙwace mulki da ƙarfi da aka yi a ƙasar.

Kazalika ya ce ya tura saƙo na musamman ga shugaba Patrice Talon, don nuna goyon baya a gare shi da kuma iyalansa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments