Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasa'Za a iya kara fuskantar juyin mulki a Afrika ta Yamma –...

‘Za a iya kara fuskantar juyin mulki a Afrika ta Yamma – Lauya Femi Falana

Sanannen lauya kuma mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya ce Najeriya za ta gaza shawo kan juyin mulki a yammacin Afrika muddin ta ki magance matsalolin cikin gida.

Ya gargadi gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu kan ta daina fada da damar fadin albarkacin baki da matsa wa ‘yan adawa.

Lauyan ya yi kira ga hukumar zabe ta kasa INEC ta bude kofa domin jam’iyyun da ke da akidar siyasa su samu damar rajista

Lauyan ya yi wannan bayanin ne lokacin da kasashen Yammacin Afrika ke sake fuskantar kalubalen juyin mulki.

Falana ya bayyana matsayarsa ne a shirin Politics Today na Channels Television, inda ya jaddada cewa matsalolin tattalin arziki, talauci, jahilci da rashin tsaro suna daga cikin manyan abubuwan da ke sa jama’a tawaye.

Ya ce idan ana son ingantacciyar dimokuradiyya, dole gwamnati ta bude sarari ga ’yancin fadin albarkacin baki, ta kare ’yancin dan kasa, kuma ta daina daukar suka a matsayin laifi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments