Saturday, October 17, 2026
HomeLabarai'Yan Bindiga sun yi garkuwa da wani Dattijo a Kano

‘Yan Bindiga sun yi garkuwa da wani Dattijo a Kano

'Yan bindigan sun yi garkuwa da wani dattijo manomi tare da jikkata ɗansa a harin da suka kai.

Wasu mutane da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari a kauyen Kururawa da ke yankin Lakwaya, karamar hukumar Gwarzo, jihar Kano.

‘Yan bindiga na ci gaba da yin kutse daga Katsina zuwa wasu kauyukan jihar Kano, inda suke addabar mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Mazauna yankin sun nuna damuwa kan hare-haren ‘yan bindiga, inda suka yi kira ga gwamnatin Kano kan ta kawo musu daukin gaggawa

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments