Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa zamanin layukan man fetur ya ƙare, yayin da Kirsimeti ke tafe.
Da yake magana bayan ganawarsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban Ƙasa, Dangote ya ce masana’antarsu ta riga ta sanar da hukumar kula da man fetur ta Najeriya cewa tana iya samar da lita miliyan 50 na man fetur a kullum.
Ya ce wannan ne karo na farko tun 1972 da Najeriya za ta kawar da matsalar karancin mai, ba ta hanyar shigo da shi daga waje ba—sai dai ta hanyar samarwa a cikin gida.
A cewarsa, daga watan Fabrairu, matatarsa za ta rika samar da lita miliyan 15 zuwa 20 – fiye da buƙatar Najeriya, wanda hakan zai ba su damar sayarwa ƙasashe makwabta, kuma su ma ba za su ƙara fama da karancin mai ba.
Ya ce wannan ci gaban zai taimaka wa masana’antun cikin gida, musamman masu sarrafa robobi, waɗanda a baya suke kashe kusan Dala miliyan 400 duk shekara wajen shigo da kayan amfani daga waje.