Sabon ministan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa mai ritaya ya buƙaci ilahirin ma’aikatan da ke ƙarƙashinsa masu kaki da fararen hula da su yi amfani da dukkanin matakan da suka dace a yaƙi da ayyukan ta’addanci ba tare da jiran umarni ba.
Yayin jawabinsa na farko bayan isa ofishi a shalkwatar tsaron Najeriya da ke Abuja jiya Juma’a, Musa ya sake nanata alwashinsa na gaggauta ɗaukar matakan da suka kamata wajen murƙushe barazanar tsaron da ƙasar ke fuskanta tare da gabatar da sababbin tsare-tsaren da za su samar da daidaito ga jama’ar ƙasa ta fuskar tsaro.
Janar Musa mai ritaya, wanda kafin yanzu shi ne babban hafsan tsaron Najeriya ya bayyana cewa da yarda da shugaban ƙasar ya yi masa da kuma cikakken goyon bayan jama’a ne ya dawo da shi aiki a matsayin ma’aikaci, a don haka babban aikin da ke gabansa shi ne ɗaukar matakan gaggawa da suka kamata wajen magance matsalolin tsaron ƙasar.
Tuni dai Janar Christopher Musa ya sanar da wasu sababbin tsare-tsare daga cikin matakan da zai ɗauka a ƙoƙarin yaƙi da matsalolin tsaron da suka yiwa Najeriya katutu ciki har da janye ilahirin sojojin da ke shingayen bincike tare da tura su dazuka don tunƙarar ƴan ta’addan.