Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeDonald Trump ya yi nasarar lashe kyautar zaman lafiya ta FIFA

Donald Trump ya yi nasarar lashe kyautar zaman lafiya ta FIFA

Shugaban Amurka Donald Trump ya lashe sabuwar kyautar zaman lafiya ta hukumar ƙwallon ƙafa ta FIFA, wato FIFA peace prize.

FIFA ta ce ta ba Trump wannan lambar yabo ne sanadiyyar rawar da ya taka wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya.

An bai wa Trump lambar yabon mai launin zinare, hannuwa riƙe da duniya a sama.

An dai gudanar da bikin raba jaddawalin gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta duniya a cibiyar John F Kennedy da ke birnin Washington na ƙasar Amurka.

Yayin da ya rage saura ƙasa da kwana 200 a fara gasar, kowace ƙasa ta zura ido ta ga ƙasashen da za ta kara da su.

A wannan Karon dai ƙasashe 48 ne za su kara a gasar, a maimakon 32 da suke bugawa a baya.

Za a samu rukuni 12, kowane ƙunshe da ƙasashe hudu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments