Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiDokar hana goyo ba ta shafi masu akin gida da jigilar kaya...

Dokar hana goyo ba ta shafi masu akin gida da jigilar kaya ba –Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa dokar hana goyo a Babura ba zai shafi mutanen da ke amfani da babur wajen jigilar kaya da kuma aikin gida ba, kamar kai yara makaranta da sauransu

Gwamnati ta yi bayanin ne don rage wa jama’a radadin dokar tare da kare masu sana’ar jigilar kaya.

Tashar Kwankwasiyya Reporters ta rawaito cewa Kwamishinan Shari’a na jihar, Abdulkarim Kabir Maude, SAN, ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da ya yi da Kwamishinan ’yan sanda na Kano.

Ganawar ta mayar da hankali ne kan matsalolin da jama’a suka fuskanta bayan gwamnatin Jihar ta fara aiwatar da dokar hana goyo a babura a wasu sassan jihar.

Kwamishinan ya bayyana cewa an tattauna korafe-korafe da dama da al’umma suka gabatar, yayin da bangarorin biyu suka cimma matsaya a kan yadda za a aiwatar da dokar ba tare da tauye hakkin masu jigilar kaya da babur ba.

Ya bukaci jama’a da su guji sabawa doka sannan kuma su cigaba da hade Kai da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankunan da dokar ta shafa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments