Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta rasu a asibitin haihuwa da kula da yara na Turai Umaru Musa Yar’adua da ke jihar Katsina, bayan zargin cewa wani ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a turo kudin amfani da iskar ‘oxygen’ ta waya, inda ya nace dole sai sun kawo kuɗi a hannu.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin bayan da aka kai matar cikin mawuyacin hali, tana buƙatar gaggawar samun iska da zai taimaka mata wajen numfashi.
Wani ganau ya bayyana wa gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a cewa mai karɓar kuɗi na asibitin ya ƙi yarda a tura kuɗi ta waya inda ya ce dokar asibitin ba ta yarda da hakan ba, kuma dole ne su bi umarni.
Wani mutum da ya yi ƙoƙarin shiga tsakani ya roƙi mai karɓar kuɗin da ya amince a tura masa kuɗin ta waya domin a ceto rayuwar matar amma ya ƙi, ganin halin da matar ke ciki, sai ya yi alƙawarin biyan kuɗin har da ƙarin har ya fito da dala 100 ya miƙa wa ma’aikacin, amma duk da haka yaƙi.
Ya bayyana abin da ya faru a matsayin “mai matuƙar tayar da hankali,” inda yace matar ta rika kuka tana neman taimako har sai da ta mutu da misalin ƙarfe 11:30 na dare.
Amma kuma, asibitin sun ce ba su karɓi takardar koke kai tsaye daga jama’a ba game da lamarin, sai dai ta hannun wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam, IHRAAC.