Hukumar alhazai ta kasa, NAHCON, ta sanar da jerin sababbin ka’idoji da matakai game da aikin Hajjin 2026.
Hukumar ta kuma umarci kamfanonin jirage da su fara ba wa mahajjata tikitin tafiya tun kafin lokacin tashinsu domin rage matsaloli.
Sababbin dokokin da hukumar aikin Hajji ta kasa ta samar sun tanadi hukunci mai tsanani ga duk mahajjacin da ya rasa jirginsa wajen tafiya.
NAHCON ta kuma bukaci bin sharuddan kiwon lafiya na Saudiyya, ciki har da cututtuka da za su iya hana mahajjaci tafiya zuwa aikin hajjin.
An bayyana sabon tsari ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a jiya 4 ga watan Disamba, 2025, bayan wani taro da aka gudanar da shugabannin alhazai na jihohi da manyan kamfanonin jiragen sama.