Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci manyan hafsoshin tsaro da hukumomin tattara bayanan sirri su kara inganta dabaru da samar da sakamako mai gamsarwa a yakar matsalolin tsaro da ke addabar wasu sassan kasar.
Kiran shugaban ya biyo bayan wani muhimmin taro da ya gudanar da shugabannin tsaro a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Taron da aka gudanar a sirrance ya ɗauki fiye da sa’a guda a ranar Talata, inda shugaban ya tattauna da manyan hafsoshin soji da na na tattara bayanan sirri kan matakan da ake bukata don kawo karshen barazanar tsaro.
Da yake jawabi bayan kammala taron, babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana cewa zaman ya kasance mai matukar muhimmanci.