Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMajalisar Wakilai na shirin fitar da matsaya game da kirkirar sababbin Jihohi...

Majalisar Wakilai na shirin fitar da matsaya game da kirkirar sababbin Jihohi a Najeriya

Majalisa na shirin fitar da matsaya a kan samar da 'yan sandan jihohi

Majalisar Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa za ta kada kuri’a game da batun kirkirar sababbin jihohi, kafa ’yan sandan jihohi da ba wa kananan hukumomi ‘yancin kai.

Haka kuma za a duba batun kebe kujeru na musamman ga mata, a yayin da ake kara duba yadda za a yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima.

Ben Kalu, wanda shi ne shugaban kwamitin sake duba kundin tsarin mulki, ya bukaci ‘yan majalisa su kasance cikin zaman da za a yi na sake nazarin kundin kafin fitar da matsaya.

Ya ce kwamitinsu ya kammala aikin da ya dace a wannan matakin, yayin da ake shirin daukaka batun zuwa mataki na gaba da ‘yan majalisa za su bayyana matsayarsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments