Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cewa dokar hana zirga-zirgar achaba da aka kafa tun 2013 tana nan daram, domin kare tsaro da rayukan jama’a.
Kwamishinan shari’a na jihar, AbdulKarim Maude SAN, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai, inda ya ce haramcin ya fi karfi a cikin kwaryar birnin Kano musamman a kananan hukumomin Kano Municipal, Gwale, Nassarawa, Tarauni, Ungogo ta Kudu da Fagge.
Maude ya ce dokar ba sabuwa ba ce, kuma gwamnati ba za ta yi wasa da aiwatar da ita ba. Ya bayyana cewa a wasu sassan da ke wajen tsakiyar birnin an yi sassauci, amma dole masu achaba su yi rajista da mai unguwa, karamar hukuma da kuma ofishin ’yan sanda kafin su samu izini.
“Sai ya yi rajista da mai unguwa, sai kuma ya yi rajista da karamar hukuma, sannan sai ya sake rajista da ofishin ’yan sanda na yankin.”
Ya kara da cewa dokar tana nan aiki tun daga 2013 domin taimakawa tsaro da tsafta a fannin sufuri, tare da gargadin cewa hukuncin karya doka ya kasance daurin watanni shida ko tarar N10,000, ko duka biyun.
Gwamnati ta ce tana son ganin an bi doka domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.