Akalla mutum biyar ne aka kashe bayan wasu ’yan bindiga sun kai hare-hare a wasu yankuna na Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi ta Jihar Filato.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne ranar Alhamis a yankunan Sabon Angwa da ke kusa da Bet/Zat, da kuma Rakung.
An kashe mutum huɗu a Sabon Angwa, yayin da aka kashe mutum guda a Rakung. Mazauna yankin sun ce an samu gargaɗin yiwuwar harin tun kafin faruwarsa.
Sun bayyana damuwarsu kan yadda harin ya faru da misalin ƙarfe 7:22 na dare, duk da dokar hana fita da aka sanya daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.
Shugaban ƙungiyar Berom Youth Moulders Association, Dalyop Solomon Mwantiri, ya tabbatar da cewa ya sanar da hukumomin tsaro kan barazanar harin tun kafin faruwarsa. Sai dai kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Alfred Alabo, bai mayar da martani kan lamarin ba har zuwa lokacin kammala rahoton.