Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gudanar da ibadar Umrah a Masallacin Harami da ke birnin Makkah na ƙasar Saudiyya, inda ya yi addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa a Najeriya.
Kamfanin Dillancin Labaran Saudiyya (SPA) ne ya tabbatar da kammala ibadar a ranar Juma’a, 30 ga Oktoba, bayan shugaban ya isa ƙasar a ranar Alhamis.
An bayyana cewa Tinubu ya gudanar da ibadar ne domin neman shiriyar Allah da albarkarsa ga Najeriya da al’ummarta.
Addu’ar ta zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tsaro da matsalolin tattalin arziki, waɗanda ke buƙatar ƙoƙarin gwamnati da haɗin kan al’umma.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai dawo Najeriya mako mai zuwa bayan kammala ziyarar ibadar tasa a ƙasar Saudiyya.