Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce tana ƙoƙarin kawar da matsalolin da ke hana masu buƙata ta musamman, musamman masu nakasa, gudanar da zaɓe cikin sauƙi a zaɓen 2027.
Kwamishinan zaɓe na jihar Kogi, Dr. Shehu Wahab, ne ya bayyana hakan a Lokoja ranar Talata, yayin wani taron wayar da kan masu nakasa da jami’an zaɓe kan hanyoyin inganta shigar masu nakasa cikin harkokin zaɓe.
Wahab ya ce hukumar na son tabbatar da cewa duk ɗan ƙasar da ya cancanci zaɓe zai iya amfani da haƙƙinsa ba tare da fuskantar matsalolin jiki ko na tsarin gudanarwa ba. Ya ce taron zai taimaka wajen tabbatar da aiwatar da manufofin hukumar a matakin ƙananan hukumomi.
Ya ƙara da cewa INEC za ta inganta amfani da kayan taimako kamar takardun zaɓe na Braille ga makafi, na’urorin ƙara girman rubutu da fastocin wayar da kan masu nakasa. Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwa da ƙungiyoyin masu nakasa da sauran hukumomi.
A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar masu nakasa ta ƙasa a jihar, Ibrahim Arome Daniel, ya ce masu nakasa sun sha fuskantar matsalolin rashin haɗa su cikin harkokin zaɓe a baya. Ya yaba da ƙoƙarin shugabancin INEC na yanzu wajen tabbatar da cewa suna samun damar kaɗa ƙuri’unsu.
A gefe guda, daraktan Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) a jihar, Ayedime Aleku, ya shawarci masu zaɓe da su karɓi katin zaɓensu na dindindin (PVC) a ofisoshin INEC da ke hedikwatar ƙananan hukumomi 21 na jihar. Ya kuma buƙaci masu nakasa su bayyana ƙalubalen da suke fuskanta domin a samar musu da mafita kafin zaɓen 2027.