Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiYadda wani mahaifi ya rasa ’ya’yansa biyar a hatsarin tankar ruwa da...

Yadda wani mahaifi ya rasa ’ya’yansa biyar a hatsarin tankar ruwa da keke napep a Gombe

Mansur Muhammad, wani mahaifi a Gombe, ya bayyana yadda ya rasa ’ya’yansa biyar bayan wata tankar ruwa ta buge keke napep ɗin da ke kai su makaranta a safiyar Talata.

Mansur Muhammad, wani mahaifi a Gombe, ya bayyana yadda ya rasa ’ya’yansa biyar bayan wata tankar ruwa ta buge keke napep ɗin da ke kai su makaranta a safiyar Talata.

Hatsarin ya faru kusa da makarantar Kanady Academy, a yankin GRA na birnin Gombe. Yara biyar sun rasu, yayin da wasu uku suka jikkata.

Yaran da suka rasun sun haɗa da Maryam, Usman, Hauwau, Aliyu da Fatima Mansir Adamu. Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira, Umar Mansur, ya ce keep napep ɗin ya faɗi kafin tankar ruwan ta bi ta kansu.

Mansur ya ce an kira shi waya bayan mintuna kusan 40 da yaran suka bar gida, aka sanar da shi hatsarin. Da ya isa asibiti, ya ga wasu a raye, amma daga baya aka kai gawar ’ya’yansa biyar zuwa asibitin ƙwararru na Gombe.

Ya ce rashin lafiya ne ya hana shi kai yaran makaranta da kansa, lamarin da ya sa matarsa ta nemo musu keke napep. Ya tuna yadda suka yi masa bankwana suna cewa, “Abba, za mu makaranta,” bai san cewa shi ne karo na ƙarshe da zai gan su ba.

Mansur, wanda yake da ’ya’ya 12, ya ce bakwai ne suka rage masa. Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi ta’aziyya ga iyalan, tare da kira ga direbobi da su kiyaye dokokin hanya, musamman lokacin jigilar ɗalibai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments