Ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona, Lamine Yamal, ya bayyana cewa Lionel Messi zai fi sauran ’yan wasa taka rawar gani a gasar cin kofin duniya ta 2026.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Yamal ya bayyana hakan ne a wasu saƙonni da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Talata.
Haka kuma, matashin ɗan wasan ya gode wa Messi, kyaftin ɗin tawagar Argentina, bisa kiran wayar da ya yi masa da kuma nuna masa goyon baya bayan wani abin da ya bayyana a matsayin “dare mai wahala” da ya fuskanta dangane da bikin bayar da kyautar Ballon d’Or.
Yamal, wanda ke taka leda a Barcelona, na daga cikin matasan ’yan wasan da ake sa ido a kansu a fagen ƙwallon ƙafa na duniya.
Gasar cin kofin duniya ta 2026 za ta gudana a ƙasashen Amurka, Kanada da Mexico, inda tawagogi daga sassa daban-daban na duniya za su fafata domin neman kofin.