Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiLabarai’Yan sanda sun kama wani matashi bisa zargin hallaka budurwarsa a jihar...

’Yan sanda sun kama wani matashi bisa zargin hallaka budurwarsa a jihar Edo

Rundunar ’yan sandan Jihar Edo ta kama wani matashi mai suna Miracle Samuel, mai shekaru 21, bisa zargin kashe budurwarsa da ya haɗu da ita a kafafen sada zumunta.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Patrick Daaor, ya ce matashin da budurwar sun shafe watanni suna tattaunawa a intanet kafin ya gayyace ta gidansa da ke yankin Ahor a birnin Benin, inda ake zargin ya kashe ta da wuƙa.

Sai dai wanda ake zargin ya ce bai yi niyyar kashe ta ba, yana mai cewa sun samu saɓani ne, inda ta ɗauki wuƙa da niyyar caka masa. Ya ce sun yi kokawa kan wuƙar, a lokacin ne ta samu rauni a wuya.

Miracle ya ƙara da cewa ya yi ƙoƙarin taimaka mata bayan ta ji rauni, amma ta mutu. Rundunar ’yan sanda ta ce yana tsare a hannunta, kuma za a gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments