Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa jam’iyyar na shirin haɗa kai da wasu jam’iyyun siyasa domin ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2027.
Yilwatda ya bayyana hakan ne ranar Asabar, yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Jihar Kaduna.
Yilwatda ya ce jam’iyyun Accord, PDP da APGA sun haɗa kai da APC domin goyon bayan sake zaɓen Tinubu.
Sai dai, wannan ikirari na buƙatar ƙarin bayani kan irin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin jam’iyyun.
Shugaban APC ɗin ya kuma yi ikirarin cewa mata da matasa na nuna goyon baya ga shugabancin Tinubu, yana mai cewa manufofin shugaban ƙasar na ba su ƙwarin gwiwa.
Ya bayyana cewa APC za ta mayar da hankali wajen yaƙin neman zaɓenta kan ayyukan da gwamnatin Tinubu ta gudanar da kuma gyare-gyaren tattalin arzikin da take aiwatarwa.
Yilwatda ya nuna kwarin gwiwar cewa gyare-gyaren za su haifar da sakamako mai kyau, yana mai cewa wa’adin farko na Tinubu ya kafa tubalin gina Najeriya mai wadata da tsaro.